Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna ta kama mutum 157 bisa zargin fashi, garkuwa da mutane satar kayan tallafin coronavirus.
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Umar Muri yayin bayyana sakamakon binciken da suka gudanar, ya ce an kama mutanen dauke da bindigogi 24 kirar AK47, kananan bindigogi uku, kirar hannu guda daya, harsasai, da sauran muggan makamai.
- An cafke masu fyade 14 a Kaduna
- Hukuma ta sasanta mazauna iyakar Kaduna da Filato
- ‘A kamo barayin kayan tallafin COVID-19 na Kaduna’
- Ta rasa ranta yayin wawason kayan tallafi a Kaduna
“Mun fito da sabbin dabarun yaki da muggan laifuka a Jihar Kaduna, saboda haka muna bukatar jama’a su ci gaba da ba mu bayanan abubuwan da ke faruwa domin dakile miyagun ayyuka.
“Ina amfani da wannan dama wajen jinjina wa matasan da suka gudanar da zanga-zangar #EndSARS da #ProSARS a Kaduna, cikin lumana ba tare da bata kayan gwamnati da na al’ummar gari ba yadda aka yi a wasu jihohi”, inji CP Muri.
Muri ya ce sabbin hanyoyin yaki da aikata laifuka a jihar ne ya kawo saukin tashe-tashen hankula da ake samu a wasu yankunan jihar, da suka hada da Zangon-Kataf, Giwa, Chikun, Kaura, Kaura.
Ya ce, “Ya kamata mutane su fahimci cewa don an soke SARS an kafa SWAT ba ya nufin za a debo ’yan sandan da aka samu laifin zaluntar mutane a sa su cikin sabuwar tawagar rundunar”, inji shi.
Ya ja hankalin mutane su ci gaba da ba wa ’yan sanda hadin kai domin kawo gyara, tare da maganin bata-garin da ke cikin hukumar.