Rundunar ‘yan sanda a Jihar Yobe ta kuɓutar da wani ƙaramin yaro mai suna Adamu Sani daga hannun masu garkuwa da mutane.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan, DSP Dungus Abdulkareem ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Damaturu, babban birnin Jihar Yobe.
- Atiku ya yi wa Tinubu jajen auna tsautsayi a Eagle Square
- Zan aike wa majalisa ƙudirin ƙarin mafi ƙarancin albashi —Tinubu
Ya ce jami’an ‘yan sanda hedikwatar da ke Gujba ne suka kuɓutar da yaron tare da kama jagoran masu garkuwar.
Bayanai sun ce, lamarin ya faru ne a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kutsa cikin ƙauyen Bungai na garin Buni Yadi da ke Ƙaramar Hukumar Gujba.
DSP Dungus ya ce maharan sun riƙa harbi da baka da kibiya da kuma bindiga, lamarin da ya ba su damar yi wa mazauna yankin barazana tare da awon gaba da yaron mai shekara uku.
DSP Dungus ya ce a ci gaba da gudanar da ayyukan leken asiri tare da hadin gwiwar ’yan banga, an gano maboyar masu garkuwa da mutane a cikin garin Buni Yadi, inda suka fatattake su, sannan suka kama shugabansu mai suna Yau Usman tare da yaron hannunsa.
A yayin da sauran masu garkuwar suka tsere, an garzaya da yaron da aka ceto zuwa asibiti domin duba lafiyarsa.