✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘An kusa kawo karshen matsalar karancin wutar lantarki’

Aminiya: Mene ne matsalolin da kuke fuskanta?Tun daga lokacin da mu ’yan kasuwa muka karbi wannan kamfani daga hannun gwamnati mun fara da gyara ginin…

Aminiya: Mene ne matsalolin da kuke fuskanta?
Tun daga lokacin da mu ’yan kasuwa muka karbi wannan kamfani daga hannun gwamnati mun fara da gyara ginin kamfanin da ke kan Titin Neja a birnin Kano. Sannan muka tantance yawan masu amfani da wutar lantarki don gane yawan kudin da ya kamata ya shigo a kowane wata da sauransu.
Aminiya: Yaya dangantakarku da kamfanin da ke tura wutar lantarki (TCN)?
Ya dace mu kara fahimtar juna domin a da kamfani daya ne kafin aka sayar da wannan bangare, don haka muna bukatar juna don su ba mu wuta, sannan mu rarraba ga kamfanoni da gidaje. Ya kamata mu kara fahimtar juna don a gina kasa baki daya.
Aminiya: Kimamin Kilowatt nawa kuke bukata don ku raba ga jihohin Kano da Jigawa da  Katsina?
Muna samun wuta daga kimanin Kilowatt 100 zuwa 270, amma  muna son a samar mana da Kilowatt 600  don a samar da wuta a koyaushe.
Aminiya: Ko an samu ingantuwar wutar lantarki bayan da ku ’yan kasuwa kuka karbi kamfanin?
kwarai kuwa, domin wutar da muke samu a yanzu ta ninka da kashi 100, don nakan zagaya Kano ina ganin ana barin wutar lantarki a kunne da rana wadda a da sai dai a kunna janareto. An kusa kawo karshen matsalar karancin wuta, insha Allah.
Aminiya: Yaushe za a samar da mita mai kati ga jama’a?
A yanzu mun yi odar mita mai kati har guda dubu 90 a Kano sannan za a raba su ne ga wanda ya fara zuwa ya cika ka’ida, ba alfarma ba.
Aminiya: Wane sako kake da shi ga masu jifan ma’aikatanku idan sun zo yanke wuta?
Ya kamata jama’a su guji karya doka don ma’aikaci yana aikin yanke wuta dalilin ba a biya ba ne. Don wanda ya biya ba a taba wutarsa. Shi ya sa muke da burin samar da mita mai kati. Ya kamata jama’a da hukumomin tsaro su tallafa don kare kayan domin a ciyar da kasa gaba.  Sannan su fallasa wadanda ke yin haka ga hukuma.
Aminiya: Kamar nawa kuke samu a wata a Jihar Kano?
Kafin zuwanmu ana tara Naira miliyan 700, amma mu muna samun fiye da Naira biliyan daya.
Aminiya: Me za ka ce game da ziyarar duba aikinku da Hukumar Sayar da Kamfanonin Gwamnati (BPE) ke yi?
Duba aiki ya dace, domin ganin mu ’yan kasuwa mun cika alkawarin da muka yi wa gwamnati na samar da wutar lantarki ga al’umma ba tare da mun matsa musu ba, don kada mu ce mun samar da lantarki bayan ba haka ba ne.
Aminiya: Mene ne dalilin da ya sa aka biya ma’aikatanku rabin albashi a watan Satumban da ya wuce?
Dalilin haka shi ne mita mai kati ta iso, kuma za mu biya kudin fito, wannan ya sa muka biya kashi 60 kafin daga baya muka biya ragowar kashi 40.