Gwamnatin Jihar Katsina ta samu nasarar kubutar da wasu mutum 9 ’yan asalin kasar Nijar daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su.
Kwanaki tara da suka gabata ne mutanen da aka ceto suka fada komar masu ta’adar garkuwa da mutane a kauyen Bima na yankin Maradi da ke jamhuriyyar Nijar wadanda suka hada da mata hudu, maza hudu, da karamin yaro daya.
- Jonathan zai jagoranci taron Daily Trust ranar Alhamis
- Yadda ’yan bindiga suka sace Farfesa suka harbi yaransa biyu a Zariya
- ‘Babu bukatar shaidar gwajin COVID-19 daga wurin dalibai yayin komawa makaranta’
Da yake zantawa da manema labarai a fadar gwamnatin Jihar Katsina yayin karbar mutanen da aka ceto a ranar Litinin, Gwamna Aminu Bello Masari ya ce wannan nasara ta tabbata ne a sakamakon ci gaba da aikin hadin gwiwa da gwamnatinsa take yi tare da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.
“A baya da na zanta da ku, na sanar da ku a kan irin kokarin da jami’an tsaro da gwamnatin Jihar Katsina ke yi don ganin an sako duk wadanda aka yi garkuwa da su a jihar.”
“A wancan karo, mun samu kimanin mutum 144, sai kuma lokacin da nake Abuja, mun samu karin mutum 37 da aka ceto kuma aka mayar da su cibiyarsu ta Jihar Zamfara, kuma a yanzu mun sake samun mutum 9 da aka sace a Jamhuriyyar Nijar,” inji Gwamnan.
Gwamnan ya yi bayanin cewa, kwararru za su duba lafiyar mutanen da aka ceto a yanzu kuma daga bisani za a danka su a hannun jami’an hukumar Kula da Shige da Fice ta jamhuriyyar Nijar ta hannun takawararta ta Najeriya.
Ya sake jaddada cewa babu wata tattaunawa da gwamnatinsa ke yi da ’yan bindiga, sai dai sun yi amfani da irin dabarun da suka ribata wajen karbo daliban Kankara da aka kubutar a kwanakin baya.
Ya ce, “Sojoji da ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro su ne a kan gaba wajen yaki da ’yan bindigar kuma har yanzu suna kawo hari wanda hakan zai tabbatar muku da cewa babu wata yarjejeniyar sulhu da muka kulla da su,” inji Masari.
Wani daga cikin wadanda aka ceto, Issofou Ali, ya ce su goma ne aka sace a kauyen na Bima, ciki har da wata ’yar Najeriya wacce tuni ta sansanta da maharan kuma ta san inda dare ya yi mata bayan ta biya kudin fanasa, inda su kuma suka kwashe kwanaki tara a daure da sarka.
Ya ce baya ga mutane, maharan sun kuma sace dabbobi da dama yayin da suka kai farmaki kauyen da misalin karfe 11 na dare a ranar Asabar ta makon jiya.