Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya sha alwashin tabbatar da yi wa dukkan matasa masu yi wa kasa hidima a Jihar allurar rigakafin COVID-19.
Ya yi alkawarin ne ranar Asabar lokacin da Shugaban Hukumar da ke Kula da Matasa Masu yi wa Kasa Hidima (NYSC), Birgediya Janar Shu’aibu Ibrahim ya ziyarce shi a gidan gwamnatin Jihar da ke Katsina.
- ‘Bai kamata Turanci da Lissafi su zama dole wajen samun gurbin karatu ba’
- An hana sayarwa ko ba da hayar gida ko fili a Kano sai da izinin Hakimi
A cewar wata sanarwa da Daraktar Yada Labarai ta NYSC, Misis Adenike Adeyemi ta fitar, Gwamnan ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bayar da gudunmawa ga hukumar a Jihar.
Masari ya kuma umarci sakatariyar hukumar da ke Jihar da ta hada kai da Ma’aikatar Lafiya ta Jihar don samun nasarar aiwatar da shirin cikin sauki.
“Gwamnatin Jiharmu za ta ci gaba da bayar da kowanne irin hadin kai da goyon baya ga shirin yi wa kasa hidima,” inji shi.
Tun da farko, shugaban na NYSC, Birgediya Janar Shu’aibu ya mika godiyarsa ga Gwamnan kan irin gudunmawar da hukumarsa ta samu daga Gwamnatin Jihar.
Ya ce daga cikin gudunmawar akwai gyara dakunan kwanan matasa da kuma cibiyar koyar da sana’o’i da ke sansanin bayar da horo ga matasan da ke Jihar.
Ya kuma yi alkawarin ci gaba da kulla kyakkyawar alaka tsakanin hukumarsa da Jihar ta Katsina. (NAN)