✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kubutar da Sanata Iyabo daga masu garkuwa

Rundunar tsaro wacce jami’an soji da na farin kaya suka rufa wa baya, ta yi nasarar kubutar da Sanata Iyabo Anisulowo, tsohuwar minister a Maikatar…

Rundunar tsaro wacce jami’an soji da na farin kaya suka rufa wa baya, ta yi nasarar kubutar da Sanata Iyabo Anisulowo, tsohuwar minister a Maikatar Ilimi ta tarayya, kwanaki shida da yin garkuwa da ita.
Gwamnan Jihar Ogun, Sanata Ibikunle Amusun ya shaida cewa an kame mutum biyu cikin wadanda ake zargi da shirya garkuwar. “Tun da fari sun nemi a ba su kudin fansa Naira miliyan 100, da suka ga na shiga cikin lamarin sai suka rubanya kudin zuwa Naira miliyan 200. A lokacin da nake kokarin tattaunawa da su, sun ci mutuncina kwarai, babu irin zagin da ba su yi mini ba, sai dai a yanzu cikin yardar Allah ga su nan a hannu, ba kuma mu ba su ko sisin kwabo ba da sunan kudin fansa.” Inji gwamnan.
Ya yaba wa kokarin jami’an tsaron da suka hada karfi da karfe suka kubutar da ita, abin da ya ce mudin za a ci gaba da samun irin haka; za a kawo karshen matsalar yin garkuwa da jama’a a daukacin ƙasar nan.
A nasa bangaren, Kwamishinan ’yan sandan jihar, Abdulmajid Ali wanda ya jagoranci samamen, gode wa Allah ya yi bisa nasarar da suka samu. Ya kuma danganta nasarar da irin daukin da suka samu daga Abuja na cikekken kayan aiki, kamar su jirage masu saukar angulu, wadanda suka taimaka masu a lokacin samamen.
Sanata Iyabo Anisulowo ta yaba da yadda gwamnati ta dauki kwararan matakan kubutar da ita, ta kuma yaba da kwazon rundunar tsaron da suka kubutar da ita cikin koshin lafiya.