’Yan sanda a Jihar Zamfara sun ceto wani mai suna Abdulrahman Abubakar, bayan da aka yi garkuwa da shi a Jihar Kebbi.
Mai magana da yawun ’yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, shi ne ya bayyana haka ranar Lahadi a Gusau, babban birnin jihar.
“Ranar 10 ga Fabrairu jami’an da ke sintiri a babbar hanyar Tsaf-Kucheri-Yankara suka ceto Abdulrahman Abubakar, dan shekara 20, kuma dan asalin Masarautar Gwandu a Jihar Kebbi.
“Ceto matashin bangare ne na kokarin da rundunar ke yi na yaki da garkuwa da sauran manyan laifuka a jihar.
“Matashin ya fada wa ’yan sanda daga garin Gwandu a Jihar Kebbi wasu suka sace shi a kan babur,” in ji Shehu.
A cewarsa, matashin ya ce an dauke shi zuwa wani daji inda ya shafe kwana uku a hannun masu garkuwar.
Shehu ya ce bayan kubutar da shi, an garzaya da matashin zuwa ofishin ’yan sanda don duba lafiyarsa kafin daga bisani aka sake hada shi da ’yan uwansa.
Jami’in ya ce kwamishinan ’yan sandan jihar, Mista Kolo Yusuf, ya ba da tabbacin rundunar za ta ba da himma don ganin ta kubutar da sauran mutanen da ke hannun ’yan ta’addar, da kuma ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin ’yan jihar.
(NAN)