Wani matashi a Kano ya yi zaman dirshen a cikin kwata cewa ba zai fito ba sai Shugaba Buhari ya sauka daga mulki.
Tun kusan karfe bakwai na Magaribar ranar Litinin matashin ya shige kwatar a unguwar Kabara kuma ba a iya fitar da shi ba sai kusan karfe biyu na dare.
Shaidu sun ce mutanen da ke wurin sun yi kusan awa shida suna dauki ba dadi domin su fitar da matashin daga cikin kwatar amma ya yi kememe.
Sun ce jamia’n tsaro na NSCDC (Civil Defence) da ’yan kwana-kwana da suka je wurin ma sun yi ta artabu da matashin amma ya gagara ciruwa daga kwatar.
Daga baya ’yan sanda daga rundunar rundunar Kan ka ce Kwabo da ke Kano suka je da nufin lallashi matashin da kuma kubutar da shi.
Kakin Rundunar ’Yan Sandan, Kano Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce bayan tsawon lokaci ana lallabashin matashin amma ya ki fitowa sai ’yan sanda suka yi kukan kura suka shiga cikin ramin suka fito da shi.
Wasu shaidu sun ce matashin ya shiga kwatar ce cewa ba zai fito ba har sai Buhari ya sauka daga mulki.
Amma Kiyawa ya ce bayan sun fito da shi sun yi masa wanka sun fara yi masa tambayoyi sai dai sun fahince kamar yana da tabin hankali.
Zuwa lokacin samun wannan rahoto, jami’in ya ce tuni aka fara gudanar da bincike a kan matashin wanda ba a bayyana sunansa ba.