✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kori ’yan sanda 7 daga aiki kan yi wa jama’a kwace

Jami'an da lamarin ya shafa na amfani da na'urar POS wajen karbe wa jama'a kudade

Wasu ’yan sanda da ke yawo da na’urar cirar kudi ta POS suna kwatar kudade daga hannun mutane sun rasa aikinsu.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Imo, Mohammed Barde, ya ce jami’an da aka kora su bakwai sukan kama mutane su tafi da su a wata mota zuwa wasu wurare na musamman su kwace musu kudade.

Ya ce dubun jami’an da aka kora ta cika ne bayan rundunar ta samu korafi daga jama’ar gari kan abin suke aikatawa.

Ya shaida wa manema labarai ranar Alhamis a Owerri, baban birnin jihar, cewa an gano jami’an sukan yi sintiri dauke da na’urar cirar kudi tat POS, wadda suke amfani da ita wajen karbar kudi daga asusun bankin mutanen da suka kama.