✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kori kwamandan Hisbah da aka kama da matar aure a otal

An tabbatar da laifin kwamandan Hukumar wanda ya yi fice wajen kamen karuwai.

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta sallami wani jami’inta da aka kama tare da wata matar aure a dakin otal.

Kakakin Hukumar, Lawal Fagge ya shaida wa Aminiya cewa an sallami kwamandan ne daga aiki bayan samun sa da laifin alaka da matar auren da aka kama shi da ita.

Ya ce kwamitin binciken da Hukumar ta kafa kan zargin ya tabbatar da lafin da ake tuhumar kwamandan, wanda a baya ya yi fice wurin kamen karuwai ’yan mata masu yawon bariki a garin Kano.

A baya Aminiya ta kawo rahoto cewa an rita kwamandan na Hisbah da matar auren ne a wani dakin otal da ke unguwar Sabon Gari.

Sai dai a lokacin, ’yan sanda sun nemi sanin abin da suke yi, inda ya shaida musu cewa ’yar dan uwansa ce aka kama wa masauki a otal saboda matsalar da ta samu da mijinta, kafin a shawo kan lamarin.

Tun a lokacin ne Hukumar ta kafa kwamitin binciken, wanda a yanzu ya tabbatar da laifin da ake zargin kwamandan da aikatawa.

A lokacin, Shugaban Hukumar, Ustaz Harun Muhammad Ibn Sina ya ce, “Mun kafa kwamitin mutum biyar domin bincikar lamarin, in har aka same shi da laifi to zai fuskanci hukunci.”

%d bloggers like this: