Hukumar Aikin Dan Sanda ta Najeriya (PSC) ta kori wasu hafsoshin ’yan sanda uku da kuma rage wa wasu biyar matsayi, saboda laifukan da suka aikata.
An kuma yi wa wasu hafsoshin ’yan sanda 20 gargadi bayan samun su da laifuka daban-daban, kamar yadda kakakin hukumar, Ikechukwu Ani ya sanar a ranar Laraba.
- Saudiyya ta kwashe ’yan Najeriya da suka makale a Sudan zuwa kasarta
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Hana Mata Samun Nasara A Zaben 2023
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa hafsoshin ’yan sanda da aka kora, dukkansu masu matasyin Mataimakin Surtanda (ASP) ne.
Wadanda aka rage wa matsayi kuma sun hada da wani Mataimakin Kwamishina da wani Babban Surtandan Dan Sanda (CSP) da wasu Sufurtanda su biyu da wani ASP daya.
Gargadi mai tsaurin kuma an yi ne ga wani Mataimakin Kwamishina da wasu CSP hudu da sufurtanda hudu da DSP biyu da kuma ASP 12.
Ikechukwu Ani ya ce an yanke hukuncin ne a zaman Babban Zauren Hukumar karo na 20 wanda shugabanta, tsohon Shugaban ’Yan Sandan Najeriya Solomon Arase, ya jagoranta.
Ya bayyana cewa a yayin zaman, hukumar ta amince da karin girma ga wasu manyan hafsoshin ’yan sanda 109.