✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kone gidaje a artabu tsakanin jami’an tsaro da ’yan IPOB a Imo

Ana fargabar mutane da dama sun mutu sannan an kone dukiyoyi masu yawa bayan wata taho-mu-gama da aka yi tsakanin ’yan IPOB da jami’an tsaro.

Ana fargabar mutane da dama sun mutu sannan an kone dukiyoyi masu yawa bayan dauki ba dadin da aka yi tsakanin ’yan Tawayen Fafutukar Kafa Kasar Biafra ta IPOB da jami’an tsaro.

Lamarin dai ya faru ne a garin Orlu na Jihar Imo, sakamakon wani rikici ya samo asali a makon jiya inda aka ba hammata iska tsakanin ’yan kungiyar da jami’an sojoji da na ’yan sanda.

Wasu shaguna da aka kona a kasuwar Orlu a lokacin rikicin.

Wasu rahotannin sun kuma ce a sakamakon harin, an sami rasa ran wasu daga cikin jami’an tsaron.

Wani sashe na Kasuwar Orlu da aka kona a sakamon tarzomar.

Sai dai suma yanzu haka an ce suna nan sun kuduri aniyar daukar fansa a kan ’yan tawayen.

%d bloggers like this: