Wasu da ba a san ko su wane ne ba sun kona wata gonar shinkafa mai girman akalla hekta 40 kurmus a yankin Ibadan, hedikwatar Jihar Oyo.
A kan haka ne Kungiyar Hakimai da Dagattai da Masu Unguwanni a Masarautar Ibadan ta yi kira da babbar murya ga mahukuntan jihar su hanzarta daukar matakin hukunta duk masu hannu wajen kona gonar.
Kungiyar da hadin guiwar masu ruwa da tsaki ta yi wannan kira ne cikin wata sanarwa da ta raba wa ’yan jarida a ranar Litinin.
Sanarwar mai dauke da sanya hannun shugaban kungiyar, Mogaji Asimiyu Ariori da Kodineto na Kungiyar Zaman Lafiya ta Ibadan, Mogaji Nurudeen Akinade, ta yi zargin cewa wasu makiyaya ne suka kona gonar bayan takaddama tsakaninsu da ’yan bijilante da suka hana su yin kiwo a cikin gonar.
- Najeriya A Yau: Yadda Za A Ceto Najeriya Daga Mawuyacin Hali
- Tsadar rayuwa: Bankin Afirka ya tallafawa Najeriya da dala miliyan 540
Kungiyar ta ce a baya an sha samun kone-konen gonaki a masarautar Ibadan, amma yanzu lamarin ya kazanta, inda aka kona wannan gonar shinkafa mallakar Dammy Farm a garin Ago-Amodu da ke yakin Shaki.
Kungiyar ta nuna takaicinta game da lamarin a irin wannan lokaci na tsadar rayuwa da tashin farashin kayan abinci.
Saboda haka ta ja kunnen dukkan masu aikata irin wannan danyen aiki su bar Jihar Oyo domin a cewarta ba za ta zura ido tana kallon irin tabargazar da ake tafkawa a gonakin noman kayan abinci da zai janyo karuwar farashin kayan abinci a jihar ba.
Ta roki gwamnati ta hanzarta daukar matakin kama dukkan mai laifi da tabbatar da hukunta shi.