An kona wani fasinja kurmus a cikin wata mota bayan umarnin zaman gida da haramtacciyar kungiyar IPOB ta bayar a yankin Kudu masu Gashin Najeriya ya rikide zuwa tashin hankali.
Fasinjan ya makale a ne cikin daya daga cikin motocin bas din da suka fito daga garin Umuahia na Jihar Abia, a lokacin da fusatattun magoya bayan haramtacciyar kungiyar suka ritsa su a unguwar Nkwogu, da ke Karamar Hukumar Ahiazu Mbaise ta Jihar Imo a safiyar Litinin.
- Kotu ta sa a rataye mutumin da ya kashe matarsa
- Barcelona ta maka PSG a kotu don dakile kulla yarjejeniya da Messi
’Yan IPOB din harbi direban motar a kugu, sannan suka harbe tayoyin motar; Ganin haka sai fasinjojin suka ce fara guduwa domin tsira da rayukansu, daga baya masu boren suka cinna wa motar wuta.
Umarnin na IPOB ya tsayar da harkokin kasuwanci da kuma rufe makarantu, da kuma hana gudanar jarbawar kammala sakandare na NECO da dalibai ke kan rubutawa.
A baya-bayan nan IPOB ta kai farmaki da dama a Jihar Imo, inda ta kai munanan hare-hare tare da kashe jami’an tsaro da kona ofisoshin ’yan sanda da sauran gine-ginen gwamnati.
Wakilinmu ya ce an yi ta jin karar luguden wuta a yankin Banana Junction da ke kan hanyar Orlu zuwa Owerri, a lokacin da ’yan bindiga suka yi musayar wuta da jami’an tsaro.
Mun yi kokarin samun karin bayani daga kakakin ’yan sandan Jihar Imo, CSP Mike Abattam, amma bai amsa kiran wayar da muka yi masa ba.