Wata tawagar masana kimiyya ta sanar da sarrafa kwayar magani ta kayyade iyali da maza za su rika sha.
Masanan daga Jami’ar Minnesota ta Amurka sun ce gwajin kwayar maganin hana daukar ciki na maza ya nuna gagarumin tasiri na kashi 99 cikin 100 ga namijin bera.
- Garba Shehu ya tura sakon daukar aikin da aka rufe tun 2021
- Birtaniya ta amince Chelsea ta sayar da tikitin kallon wasanni
A cikin sanarwar da masu binciken suka fitar a ranar Laraba, sun ce zuwa karshen wannan shekarar ta 2022 suke sa ran fara gwajin kwayar maganin ga dan Adam.
Gidan Rediyon Jamus ya ruwaito cewa wannan shi ne matakin da masu fafutukar daidaita jinsi suka jima suna maraba da shi.
A yayin da galibi dai mata na iya shan kwayoyi daban-daban tare da amfani da wasu tarin dabaru a kimiyyance wajen hana daukar ciki, maza dabara daya ce suke da ita – ita ce ta hanyar amfani da kwaroron roba wanda mafi akasari ake samun akasin biyan bukatar da aka nufata.
Tun daga shekarun 1960, lokacin da kwayoyin kayyade iyali na mata suka shiga kasuwa, masana kimiyya suke ta fadi-tashin ganin sun samar da wasu kwayoyin magani da maza za su rika sha domin hana daukar ciki.