An kebe mutum bakwai a babban asibitin garin Damaturu da ke cikin jihar Yobe kan zargin kamuwa da cutar Lassa a jihar.
Kwamishinan Lafiya na jihar, Bello Kawuwa shi ne ya yi furucin yayin da yake tattauna wa da Aminiya, a jhar Yobe.
“An sallami mutum uku daga cikin mutum bakwai da aka kebe bayan an gudanar da bincike a kansu sannan kuma ana ci gaba da lura da mutum hudu don a tantance su”. Inji shi
Ya ce binciken farko har yanzu bai nuna matsayin mutum hudun ba shi ya sa aka sake yi musu gwaji a karo na biyu.
“A cikin watan Juli an samu rahoton zargin bullar cutar Lassa ga mutane bakwai a Yobe kuma an gudanar da bincike a kansu kuma cikin mutum bakwai an samu uku da alamun cutar da ba ta kai cutar Lassa ba. Tuni aka gudanar da bincike don tabbatar da lamarin kuma za a tabbatar ne kawai idan sakamakon binciken ya fito” Inji shi.
Kwamishinan ya bayyana cewa tuni aka tura jami’an tawagar agajin gaggawa kan annoba zuwa yankunan daban-daban don gudanar bincike tare da wayar da kan jama’a kan cutar.