Gwmnatin Tarayya ta ba wa makarantu masu zaman kansu wa’adin 29 ga watan Yuli su cika sharuddan da ta sanya musu kafin ta sanar da ranar bude makarantu.
Minista a Ma’aikatar Ilimi Chukwuemeka Nwajiuba ya umarci makarantun su yi wa kawunansu hisabi kan yadda suka cika ka’idojin, su mika wa ma’ikatun ilimin jihohinsu rahoto kafin ranar.
“Daga nan za a zauna da masu ruwa da tsaki a yi nazarin halin da ake ciki domin yanke hukunci game da lokacin bude makarantun”, inji sanarwar da ma’aikatar ta fitar.
Nwajiuba ya ce masu ruwa da tsakin a fannin ilimi da Hukumar Jarabawa ta Yammacin Afrika (WAEC) sun amince su tattauna da wasu kasashe hudu kan sanya sabon lokacin gudanar da jarabawar WAEC a kasashen.
Najeriya ta jingine bude makarantu bayan rufe su saboda bullar coronavirus tana mai cewa dalibai masu kammala karatun sakandare ba za su yi jarabawar WAEC kamar yadda aka tsara ba har sai an tabbatar da kariyarsu daga cutar.
Sanarwar da ma’aikatar ilimin ta fitar ta ce an tsara ka’idojin bude makarantun ne da hadin gwiwar Ma’aikatar Lafiya da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) da sauran amsu ruwa da tsaki a harkar ilimi.
Sabbin ka’idojin sun hada da tabbatar da dalibai sun ci gaba da karatu ta hanyar zamani, bayan horas da malamai da kuma samar da na’urori da za su ba wa daliban damar halartar darussan daga gidajensu.
Daga nan ma’aikatun ilimi na tarayya da jihohi za su yanke hukuncin bude makarantu bayan ganawa da Kwamitin Shugaban Kasa kan Yaki da Cutar COVID-19 kan matakan kariyar cutar da na bayar da tazara da makarantu suka dauka.
Za kuma rika lura da yadda ake gudanarwa da tabbatar da wanzuwar kayan kare lafiya da aka samar a makarantun.