Takaddama ta barke bayan ’yar jaridar kafar yada labarai ta Al Jazeera Shereen Abu Aqleh ta rasu bayan an harbe ta a wani samamen da sojojin Isra’ila suka kai yankin Jenin da ke Yammacin Kogin Jordan.
Aljazeera da gwamnatin Palasdinawa na zargin dakarun Isra’ila da kashe shereen mai shekara 51 da gangan ba tare da wani dalili ba, baya ga wani dan jarida da jami’an tsaron suka jikkata, duk da cewa suna sanye da kayan sulken ’yan jarida da kowa ya sani.
- Bom ya tashi a kusa da barikin sojoji a Jalingo
- Yadda takarar ministoci ke shafar ayyuka a ma’aikatun gwamnati
Ma’aikatar Lafiya ta Palasdinawa ta ce an kai Shereen ta rasu a asibitin da aka garzaya da ita bayan dakarun Isra’ila sun harbe ta a fuska.
Ma’aiakatar tsaron Isra’ila ta musanta zargin, tana mai cewa akwai yiwuwar “harsashin mayakan Palasdinawa ya ne ya sami ’yan jaridar a lokacin da bangarorin ke musayar wuta.”
A cewara, “Wajibi ne ’yan jarida su samu kariya idan ana rikici, kuma wannan nauyi ne da ya rataya kanmu baki daya,” .
Mataimakin Ministan kasar Qatar, mamallakan kafar Aljazeera, Lolwah al-Khater ya ce an harbi Shereen ne a fuska duk da cewa ta sanya rigar da hular sulke da ke nuna ceaw ‘yar jarida ce.