Sojojin Najeriya sun kashe ’yan ta’addan ISWAP da Boko Haram akalla 48, ciki har da manyan kwamandojinsu shida a cikin mako biyu da suka gabata a yankin Arewa maso Gabas.
Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta ce a tsawon lokacin, mayakan kungiyoyin da iyalansu mutum 3,858 sun mika wuya bayan sojoji sun tsananta yi musu luguden wuta a maboyarsu a yankin, inda suka cafke manyan kwamnadojinsu da wasu mata da ke yi wa kungiyoyin fatauci.
- NAJERIYA A YA: Yadda Muka Rayu Kwana 100 A Hannun ’Yan Bindiga
- An gano kabari mai mutum 8,000 da dakarun Hitler suka kashe a Poland
“Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 42, suka cafke wasu 10 tare da kwace bindigogi kirar AK47 guda 17 da bindigar QTC rifle guda daya da bom da bindigar harba RPG daya-daya, sai kuma gurneti guda biyar da albarusai 174,” in ji kakakin Rundunar Tsaro, Manjo-Janar Onyeuko.
Ya bayyana cewa a ranar Litinin jiragen yaki sun kashe ’yan ta’adda akalla 21 a yankunan Tumbum Jaki da Tumbum Murhu da ke kusa da Tafkin Chadi a Jihar Borno.
Ya ce sojoji sun kuma kashe ’yan ta’adda da ba a san adadinsu ba a kauyen Gamage na Karamar Hukumar Dikwa da kuma a hanyar Dikwa zuwa Gamborou-Ngala da kuma titin Pulka zuwa Gwale a Jihar Borno a tsawon lokacin.
Onyeuko ya ce wasu kwamandoji ’yan ta’adda shida kuma sun mika wuya a Gwoza, an kuma cafke wasu mata biyu da ke kai wa ’yan ta’addan kayan masarufi da sauran bukatu.
Kwamandojin ’yan ta’addan da suka mika wuya su ne: Mala Hassan (Wali) da Ali Madagali (Munzur) da Musa Bashir (Chief Anur), Buba Dahiru (Munzur), Jafar Hamma (Kaid) da kuma Abbali Polisawa.
Da yake bayani a Abuja kan ayyukan sojojin na yaki da ta’addanci, Manjo-Janar Onyeuko, ya ce, ce wadanda suka mika wuyan sun hada da maza 505 da mata 1,042 da kuma kananan yara 2,311.
Onyeuko ya ce “Sauran makaman da sojoji suka kwace sun hada da gurneti guda biyar da albarusai 174.”
Akwai kuma bindigogi harbi-ruga guda biyar da harsasai guda 211 samfurin 7.62mm NATO da kuma samfurin 12.7 108mm.
Sai kuma abubuwan fashewa kirar gida guda biyu da kwanson albarusai 23 da dai sauransu.
Ya bayyana cewa ana tantancewa tare da daukar bayanan ’yan ta’addan da suka mika wuya tare da iyalnsu.
Makaman da aka kwace kuma an riga a hannanta su ga hukumomin da suka dace.