✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe ’yan sanda 2 yayin arangama da ’yan shi’a a Abuja

'Yan Shi'ar sun ƙwace makaman 'yan sanda tare da ƙone musu motoci uku.

Jami’an ’Yan Sanda biyu sun rasa rayukansu yayin da wata arangama da ta ɓarke tsakaninsu da mabiya ɗariƙar Shi’a (IMN), a kasuwar Wuse da ke Abuja.

Kazalika, an harbe wani ɗan kasuwa mai suna Amiru, yayin da yake ƙoƙarin tserewa lokacin ta tarzomar ta tashi, inda daga bisani ya rasu a hanyar zuwa asibiti.

Rikicin dai ya fara ne lokacin da ’yan Shi’a da ke gudanar da tattaki suka yi arangama da ’yan sanda.

Sun yi wa jami’an ƙawanya tare da fin su yawa, inda suka ƙwace makamansu, sannan suka ƙone motocin ’yan sanda uku.

A martanin da rundunar ’yan sandan Abuja, ta mayar kan lamarin, ta bayyana harin a matsayin abun takaici.

Amma rundunar ta tabbatar da cewa an kama mutane da dama da ke da alaƙa da rikicin.

Kwamishinan ’yan sandan Babban Birnin Tarayya, CP Benneth C. Igweh, ya yi Allah-wadai da tashin hankalin.

Ya kuma lashi takobin gurfanar da waɗanda suka aikata laifin a gaban kuliya.

Tuni dai aka shawo kan lamarin, yayain da zaman lafiya ya daidaita a yankin.