✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘An kashe ’yan sa-kai 1,773 a rikicin Boko Haram a Arewa maso Gabas’

Kungiyar ta ce na kashe mutanen ne a ts

Kungiyar ’yan sa-kai ta CJTF ta ce akalla mambobinta 1,773 da ke yaki da ’yan ta’addan Boko Haram/ISWAP ne suka mutu a Jihohin Arewa maso Gabas cikin shekara 10.

Shugaban kungiyar, Babashehu Abdulganiu ne ya bayyana hakan yayin wata hira da manema labarai a Maiduguri.

Ya ce mafi yawansu sun rasa ran nasu ne a lokacin da suke yaki da ’yan ta’addan tare da sojoji a yankunansu a dajin Sambisa da Tafkin Chadi.

Ya ce wasu daga cikinsu sun mutu ne a lokacin da suke tunkarar hare-hare a Maiduguri, wasu kuma sun fuskanci hare-haren kwantan-bauna daga ’yan ta’addan, yayin da wasu kuma suka sadaukar da rayuwarsu ta hanyar rungumar ’yan kunar bakin wake a lokacin da suke kokarin kai hari ga mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

Baba Shehu ya kara da cewa adadin mace-macen na daga cikin bayanan da suka samu a tsakanin shekarar 2012 zuwa 2022, inda ya ce duk da yawan asarar rayuka, rundunar ta CJTF ta ci gaba da jajircewa wajen ganin ta kawar ’yan kungiyar Boko Haram a jihar da kuma kawo karshen matsalar don sake  dawo da martabar jihar da ke da shi a matsayin gidan zaman lafiya a baya.

A cewarsa, CJTF kungiya ce da aka assasa ta saboda larura don kawar da munanan abubuwan da suka saba haifar da barna a cikin babban birnin Maiduguri musamman dangane da ’yan ta’addan Boko Haram.

“An fara ne a shekarar 2012, a lokacin da matasanmu suka dauki sanduna suka ce za su  yaki Boko Haram kuma mun yi nasarar fatattakar ‘yan ta’addan daga Maiduguri zuwa matsugunin su a dajin Sambisa da tafkin Chadi.”

“A shekarar 2015, gwamnatin jihar Borno ta kafa wata kungiya mai suna Borno Youths Empowerment Scheme (BOYES), inda aka sanya runduna ta hadin gwiwa ta farar hula su kimanin 23,000 a matsayin jami’an tsaro, wadanda sojoji suka horar da su sannan kuma jami’an tsaro na jihar suka tantance su.

“A yayin atisayen tantancewa, an tantance wadanda ke da hannu wajen yin amfani da muggan kwayoyi ko aikata laifuka ko wadanda aka yanke wa hukunci a baya.  Anyi hakan ne don tabbatar da cewa ba mu sake daukar  baragurbin cikinmu ba.

“Mun dauki sojoji kamar tsarin da ake da su a matsayin jagorori Sectors.  Don haka muka tura mutanenmu suka mamaye shingayen binciken abubuwan hawa tun daga sashi na daya zuwa na 10,” inji shi.

Ya kuma ce a kowanne wata, Gwamnatin Jihar Borno tana kashe Naira miliyan 150 domin biyansu kudaden alawus-alawus da kuma ba su ababen hawa da sauran kayan aiki.