Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta bayyana cewa ’yan Najeriya 614,937 aka kashe, yayin da aka sace mutum miliyan 2.2 daga watan Mayun 2023 zuwa Afrilun 2024.
Wannan na ƙunshe ne cikin rahotonta mai taken Binciken Laifuka da Tsaron Jama’a na 2024.
- Uba Sani ya mayar wa iyalan Abacha filayen da El-Rufai ya ƙwace musu
- ’Yan bindiga sun harbe malamin Jami’ar UNIZIK, sun sace motarsa
Rahoton, ya nuna cewa masu garkuwa da mutane sun karɓi jimillar kuɗi Naira tiriliyan 2.2 a matsayin kuɗin fansa, inda kowane lamari ke wakiltar kai aƙalla Naira miliyan 2.7.
Yawancin mutanen da aka yi garkuwa da su (miliyan 1.6) sun fito ne daga ƙauyuka, yayin da Yankin Arewa Maso Yamma ya fi yawan mutanen da aka sace (miliyan 1.4).
“Talakawa a karkara ne suka fi shan wahala,” in ji wani mai sharhi.
“Ko da yake an sace manyan mutane, mafi yawa daga cikin waɗanda ake garkuwa da su talakawa ne, musamman mazauna karkara.”
Rahoton, ya kuma nuna yawan kashe-kashen da aka yi, inda yankin Arewa Maso Yamma ke kan gaba da mutum 206,030, sai Arewa Maso Gabas da mutum 188,992.
A gefe guda kuws, yankin Kudu Maso Yamma shi ne yankin da ba a yi kashe-kashe da yawa ba, inda yake da mutum 15,693 kawai.
Ana kashe maƙudan kuɗi wajen biyan fansa
Rahoton ya bayyana cewa aƙalla gidaje kan kashe Naira 80,878 kan tsaro a shekarar da ta gabata, inda mazauna birane suka fi kashe kuɗi sama da na ƙauyuka.
“Mazauna birane su kan kashe Naira 86,997, yayin da mazauna karkara suke kashe Naira 72,849,” in ji rahoton.
Har ila yau, rahoton ya ce kashi 91 na sace-sacen mutane da aka yi ya faru ne domin neman kuɗin fansa, yayin da sauran garkuwa da mutanen suka shafi rikice-rikicen siyasa ko na iyali.
Yankin Kudu Maso Gabas ne, ya fi kashe kudin tsaro a gida, inda matsakaicin abin da ake kashewa ya kai Naira 135,398.
Masani ya buƙaci gwamnati ta ɗauki mataki
Wani masani kan sha’anin tsaro, Abdullahi Garba, ya yi kira ga gwamnati da ta magance matsalolin tattalin arziƙi.
Ya ce, “Masu garkuwa da mutane suna yi ne da zummar samun kuɗi daga masu arziƙi, amma talakawa ne suka fi shiga matsala.”
Ya ƙara da cewa, “Rashin daidaito tsakanin masu arziƙi da talakawa yana ƙara jefa matasa cikin aikata miyagun laifuka. Idan aka samar da ayyukan yi masu kyau, ba za su ke aikata laifi ba.”
Hukumomi ba su uffan kan rahoton ba
Ƙoƙarin samun martani daga fadar Shugaban Ƙasa, ’yan sanda da sojoji kan rahoton ya ci tura.
An yi wa wa manyan jami’ai kiraye-kirayen waya da sakonnin waya da aka aike musu, ciki har da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, amma ba su ce komai kan rahoton ba.
Matsalar tsaro dai, ita ce matsala kusan ɗaya tilo da za a ce ta fi zame wa Najeriya babbar matsala a yanzu, inda ake kashe maƙudan kuɗaɗe don ganin an kawo ƙarshenta.
Duk da ƙoƙarin da jami’an tsaro ke yi, musamman sojoji, ’yan sanda, jami’an tsaron farin kaya, amma matsalar na ci gaba da tasiri musamman a Jihohin Kaduna, Zamfara, Kebbi, Sakkwato, Neja da kuma Katsina.
Kusan kowace rana ana wayar gari da labarin hare-haren ’yan bindiga a waɗannan jihohi, wanda ke da alaƙa da satar mutane ko dabobbi kuma kisa.