Jami’an tsaro sun kashe ’yan kungiyar IPOB biyu tare da kama kwamandojinta biyu a masana’antar bom din kungiyar a Jihar Ebonyi.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ebonyi, SP Chris Anyanwu, ya ce karfin abubuwan fashewa da aka kama a masana’antar bom din zai iya tarwatsa gini da kuma kashe mutane masu dimbin yawa.
- Farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabo
- Ganduje zai sa hannu kan hukuncin rataye Abduljabbar
Ya sanar a ranar Alhamis cewa jami’an tsaron sun yi kamun ne a samamen da suka kai maboyar kungiyar mafi girma da ke yankin Obegu, a iyakar kananan hukumomin Onicha-Isu da Ishielu na jihar ta Ebonyi.
SP Chris Anyanwu ya ce jami’an hukumar tsaro ta DSS da ’yan sanda da sojoji sun bankado masana’antar bom din ne bayan sun kama wani kwamandan IPOB mai suna Sunday Ubah, wanda aka fi sani da Bongo.
Ana zargin Bongo kwamandan IPOB ne a karkashin Simon Ekpa da ke jagorantar reshen kungiyar na ESN a yankin Obegu.
Ya ce baya ga kashe ’yan kungiyar biyu a musayar wuta da cafke kwamandojinta biyu, “An kama abubuwan fashewa 30 da sinadaren hadawa da tayar da su iri-iri, hadi da bandur guda na tutocin Biafra.
“Sauran sun hada da kayan sojoji da na ’yan sanda ciki har da hayaki mai sanya hawaye da kaki da sauransu na ’yan sanda da suka kashe,” in kai shi.
Ya bayyana cewa ’yan IPOB din da suka shiga hannu na taimakawa da muhimman bayanai.