’Yan ta’addan Boko Haram sun sheka lahira, wasu akalla 135 tare da iyalansu sun mika wuya ga sojojin Najeriya a Karamar Hukumar Bama ta Jihar Borno.
Mika wuyan ’yan ta’addan ya biyo bayan karin ragargazar da sojojin rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) suke musu ne a Dajin Sambisa.
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 40 a Kebbi da Zamfara
- Hafsan dan sanda ya yi bayan gida a jikinsa a bakin aiki
“An kashe kusan ’yan ta’adda 35 a aikin hadin gwiwa a Kananar Hukumar Bama,” in ji wani kwararre a fannin yaki da tada kayar baya a Yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama.
“Akwai karin ’yan ta’adda 113 daga garuruwan Balangaje da Bula-Waziri da Bula – Kurma da Sabil – Huda wadanda suka mika wuya ga sojoji a Yamteke,” in ji shi.
Ya bayyana a Maiduguri cewa ’yan ta’addan sun ajiye makamansu ne mako guda bayan sojoji da mayakan sa-kai na Civilian Joint Task Force (CJTF) sun tsananta kai farmaki a kan maboyarsu.
Zagazola ya ce wasu karin ’yan ta’addan tare da iyalansu da suka hada da kananan yara 13 da mata daga kauyukan Nguru Soye da Kelani sun mika wuya ga sojojin Bataliya ta 202 da ke Bama.
Hakazalika, namiji daya da mata biyar da yara shida daga kauyukan Kauri da Siraja da Lene Hassana sun mika wuya ga sojoji a Mahadar Banki da ke kan hanyar Bama-Gwoza.
Ya ce duk tubabbun ’yan ta’addan na Boko Haram an mika su ga hukuma domin kula da su da kuma yin abin da ya dace da su.
Babban Kwamandan Runduna ta 7 ta Sojin Najeriya, Manjo-Janar AE Abubakar, ya jinjina wa sojojin sannan ya bukaci su fatattaki ’yan ta’addan domin dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas.