✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe wani mutum kan zargin satar mazakuta a Abuja

Daga bisani likita ya tabbatar da cewa mazakutar mutumin na nan

Wasu fusatattun mutane sun kashe wani mutum mai suna Alhaji Tijjani Yakubu bisa zarginsa da sace mazakutar wani mai suna Emmanuel Danladi da ke kauyen Kabusa a yankin Babban Birnin Tarayya Abuja.

Kwamishinan ’Yan Sandan yankin, Haruna G. Garba ne ya bayyana hakan yayin wani jawabi ga manema labarai a hedkwatar rundunar da ke Abuja, a ranar Laraba.

Ya ce jim kadan da samun samun labarin faruwar lamarin, jami’ansu sun bazama inda suka kamo wanda ake zargi da kisan da kuma wanda aka kashe din.

Kwamishinan ya ce daga bisani an garzaya da wanda aka lakada wa dukan asibiti.

“Sai dai an yi rashin sa’a, lokacin da aka garzaya da Alhaji Tijjani asibiti, inda likita da ke bakin aiki ya tabbatar da mutuwar shi. Sai dai daga bisani likitan ya tabbatar da cewa mazakutar Emmanuel din na nan, ba a sace ta ba,” in ji Kwamishinan.

Ya kuma ce yanzu haka Emmanuel din tare da wasu mutum biyu na hannunsu bisa zargin kisan mutumin, inda ya ce da zarar an kammala bincike a kansu za a gurfanar da su a gaban kuliya.

Haruna ya kuma ce makamancin irin wannan yanayin ya faru a unguwar Apo, inda suka samu kiran gaggawa cewa mutane suna shirin kashe wani mai suna Mathew Michael, sannan suka samu nasarar kwatar shi daga hannunsu.