✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

An kashe wani Musulmi saboda batanci ga Annabi a Abuja

An babbake mutumin da ransa bayan an jefe shi da duwatsu.

An kashe wani dan kungiyar ’yan banga a unguwar Lugbe da ke Abuja bisa zarginsa da yin batanci ga Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad (SAW).

Aminiya ta samu cewa wadanda suka fusata kan wannan lamari sun kashe mutumin ne a kasuwar Katako, wani bangare na kasuwar kayan marmari a rukunin Gidaje na Tarayya da ke Lugbe.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, wanda aka kashe din musulmi ne, kuma wannan ba shi ne farau ba domin an san shi da laifin cin mutuncin manzon Allah, inda na baya-bayan nan ya faru da tsakar daren ranar Asabar.

Sai dai bayanai sun ce an dauki matakin ne da misalin karfe 1 na ranar Asabar bayan ya yi kokarin neman mafaka a ofishinsu na ‘yan banga da ke kasuwar.

An tattaro cewa jama’ar da suka fusata sun ci karfin jami’an tsaron yankin, wanda a dalilin haka suka samu nasarar kashe shi a gaban ofishin, sannan suka kone shi.

“Muna san mutumin wanda ake kira Small Hundaru, wannan ba shi ne karon farko da ya zagi Annabi ba kafin a dauki matakin,” in ji Halilu, wani mai sana’a a kasuwar.

“An kama shi ne bayan ya sayi abinci a kasuwa da rana, domin a lokacin da aka yi wannan batancin mutane kadan ne a wurin, sai aka yi amfani da sanda aka buga masa kai. Duk da cewa yana da bindiga a tare da shi, an kwace ta kafin a yi masa jina-jina.

“Bayan haka, sai aka rika jifansa da duwatsu kafin ya garzaya ofishin, amma abokan aikinsa a ofishin da suka san ba za su iya kare shi ba saboda yawan mutanen da suka biyo shi, dole suka zuba ido suna kallo.

“Bayan ya sume ne aka zuba masa man fetur, aka cinna masa wuta a gaban ofishin.”

A lokacin da wakilinmu ya ziyarci wurin, ana iya ganin burbushin tayoyin da aka yi amfani da su wajen kona shi yayin da tuni ‘yan kasuwa suka kulle shagunansu don gudun abin da ka iya zuwa ya komo.

Sai dai ‘yan sanda sun hallara a wurin da tuni kura ta lafa, amma wasu bayanai na cewa ‘yan sandan sun harbi mutane uku.