✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe wani jami’i a Hukumar NFF

A wayewar garin Larabar da ta wuce ne aka samu labarin rasuwar daya daga cikin jami’an Hukumar NFF Ibrahim Abubakar a gidansa da ke Abuja. …

A wayewar garin Larabar da ta wuce ne aka samu labarin rasuwar daya daga cikin jami’an Hukumar NFF Ibrahim Abubakar a gidansa da ke Abuja.  An ce wadansu da ba a gano ko su waye ba suka halaka marigayin a gidansa da ke Abuja da tsakar daren Talata.  Har zuwa hada wannan rahoto ba a gano dalilin da ya sa barayin suka aikata wannan danyen aiki a kan marigayin ba.  Hasalima ba a tabbatar da dalilin da ya sa suka halaka shi babu gaira babu dalili ba.
A wata sanarwa da Hukumar kwallon kafa ta NFF ta fitar a yanar sardawarta na Twitter ta ce wadansu da ba a san ko wu wane ne ba ne suka kutsa gidan marigayin da tsakar daren Talata sannan suka bindige shi har lahira.
Marigayin shi ne jami’in da ke kula da harkokin tafiye-tafiye na Hukumar NFF (Protocal Officer).
Sanarwar ta nuna tuni aka yi nana’izarsa a Kaduna kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
Tuni Hukumar NFF ta aika wa iyalan mamacin sakon ta’aziyya.  Ta yi fatan Allah Ya jikansa da Rahama, su kuma iyalansa Allah Ya ba su hakurin juriyar wannan rashi da suka yi.