✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kashe shugaban ’yan bindiga Dogo Maikasuwa a Kaduna

Dogo Maikasuwa ya gamu da ajalinsa ne bayan ya dade yana ta tsere wa jami'an tsaro.

Jam’ian tsaro sun hallaka jagoran ’yan bindiga, Dogo Maikasuwa, wanda ya addabi hanyar Kaduna zuwa Kachia da al’ummomin kananan hukumomin Chikun da Kajuru na Jihar Kaduna.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce Dogo Maikasuwa ya gamu da ajalinsa ne bayan ya dade yana ta tsere wa jami’an tsaro.

“Dogo Maikasuwa, wanda aka fi sani da ‘Dogo Maimillion’ ya sha jagorantar hare-hare da sace matafiya a hanyar Kaduna-Kachia, da kauyukan kananan hukumomin Chikun da Kajuru LGAs.

“Shi ke jagorantar daya daga cikin gungun ’yan bindiga mafiya hadari a yankin, inda yake hallaka mutanen da suka sace idan an yi jinkirin biyan kudin fansa,” in ji Aruwan.

Ya ce an kwace bindiga da sauran makamai a musayar wutar da aka kashe dan ta’addan.

Ya ce ragowar sun tsere da raunin harbi a jikinsu, amma daga baya daya daga cikinsu ya mutu.