A kasar Mali an hallaka wasu manyan jami’an gwamnati biyar na kusa da Shugaban rikon gwamnatin kasar, Kanal Assimi Goita.
Rahotanni daga Bamako babban birnin kasar, sun ruwaito cewa wani harin kwantar bauna ya hallaka Oumar Traore, Shugaban Ma’aikatar Fadar Shugaban Kasa da wasu jami’an gwamnati hudu yayin da direban tawagar ya bata.
- Sevilla ta fitar da United daga Europa League
- NAJERIYA A YAU: Yadda Sabbin Ma’aurata Suka Yi Azumin Farko A Najeriya
Kafar watsa labarai ta Aljazeera ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a kauyen Nara da ke lardin Koulikoro da ke Kudu maso Yammacin kasar.
Kawo yanzu dai babu tabbacin wadanda ke da alhakin harin, amma kuma kasar Mali a yanzu kusan ita ce kan gaba wajen fama da tarzomar ’yan ta’adda a Yammacin Afirka.