✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe sama da mutane 100 a harin ƙauyen Sudan—Kwamitin

Maharan da ake fargabar sun mamaye ƙauyen, inda suka yi sanadiyyar rasa matsugunan jama’a.

Wani harin na wasu jami’an tsaro da suka kai a wani ƙauye da ke tsakiyar Sudan ya yi sanadin kashe aƙalla mutane, in ji wani kwamitin masu fafutukar kare dimokraɗiyya a ƙasar a ranar Alhamis.

Rundunar Tsaro ta (RSF), wacce ke yaƙi da sojojin gwamnati tun watan Afrilu 2023, sun kai hari ƙauyen Wad al-Noura a cikin Jihar al-Jazira ta ruwa sau biyu da manyan bindigogi a ranar Laraba, in ji Kwamitin Resistance Madani.

Sun ce maharan sun mamaye ƙauyen, inda suka yi sanadiyyar rasa matsugunan jama’a da dama.

“Kusan mutane 100 ne aka kashe,” in ji kwamitin, ɗaya daga cikin ɗaruruwan ƙungiyoyi a Sudan.”

A shafukan sada zumunta na zamani, kwamitin ya yaɗa bidiyon abin da suka ce wani kabari ne na tarin jama’a, wanda ke nuna jerin fararen likafani da aka shimfiɗa a cikin wani fili.

A cikin shekara guda, yaƙin ya kashe dubunnan mutane, ciki har da mutane 15,000 a wani gari ɗaya na yammacin Darfur.

Ƙungiyar RSF ta sha kai hare-hare tare da kai farmaki ga ɗaukacin ƙauyukan ƙasar Sudan, musamman a jihar Al-Jazira mai arzikin noma.