✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mutum uku a sabon hari a Kudancin Kaduna

Mutum uku ne suka rasa rayukansu a wani sabon hari da aka kai a kauyen Gerti da ke Gundumar Kaninkon da ke Karamar Hukumar Jama’a…

Mutum uku ne suka rasa rayukansu a wani sabon hari da aka kai a kauyen Gerti da ke Gundumar Kaninkon da ke Karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna a safiyar Litinin din makon nan.

Da yake karin bayani ta wayar tarho, Kansilan Kaninkon, Christopher Yakubu Phillip ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe takwas na safe,  kuma ya shafi wani mutum ne da dansa yayin da suke aiki a gonarsu.

Phillip, ya ce mutum na hudu da ya sha da kyar ne ya kawo labarin inda suka umarci ragowar manoman su baro gonakinsu kuma aka sanar da jami’an tsaro na sojoji suka shiga dajin inda aka gano gawarwakin wadanda aka kashe.

Kansilan ya bayyana harin a matsayin abin takaici musamman a daidai wannan lokaci da manoma ke shirye-shiryen aiki a gonakinsu. Ya yi kira ga jami’an tsaro su yi duk abin da ya kamata don kamo marasa son zaman lafiya a yankin.

Sannan ya roki gwamnati ta kara tsaurara tsaro a yankin don zakulo marasa kishi da suke aikata haka don hakan yana iya raunata harkar noma a yankin.

Wani mutumin garin da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa suna zaune a gida suka jiyo karar bindiga inda wadansu suka ce masa su shiga dajin don tabbatar da abin da ke faruwa, amma ya ce me zai kai shi cikin daji shi ba jami’in tsaro ba. “To daga baya sai muka ji labarin maharan sun kashe mutum uku a gona,” inji shi

Yayin da Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, DSP Yakubu Sabo ya ce zai kira bayan kammala zaman da suke yi amma har zuwa lokacin hada wannan rahoton bai kira ba.

A wata sabuwa kuma, an kama wani matashi da ake zargi ya sassari wata saniya a garin Ninte da ke Masarautar Godogodo da ke Karamar Hukumar Jama’a inda bayan shiga tsakani da jami’an tsaro na sojoji da ’yan sanda suka yi aka mika shi ga Dagacin Ninte da kuma Ardon Fulanin Ninte, inda aka sasanta tare da alkawarin biyan kudin barnar da ya yi kamar yadda Ardon Ninte, Alhaji Babangida Habane ya shaida wa Aminiya ta wayar tarho.

Wannan lamarin ya faru ne da misalin karfe uku na yammacin ranar Lahadin da ta gabata.