✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kashe mutum biyu, an sace malamin tsangaya da wasu da dama a Zariya

Rahiotanni sun ce 'yan bindigar sun kuma tafi da mutane da dama.

Wasu gungun ’yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai hari anguwar Kuregu da ke Wusasa a Zariya, Jihar Kaduna inda suka kashe mutum biyu sannan suka tafi da wasu da ba a san yawansu ba.

Rahotanni sun ce an kai harin ne a daren Juma’a da misalin karfe tara da rabi na dare kuma daga cikin wadanda aka tafi da su har da wani malamin tsangaya mai suna Malam Ibrahim Yakubu Umar, mai shekaru 60 a duniya.

An dai dauki tsawon lokaci yankin Wusasa bai fuskanci hari ba, in ban da wannan karon da aka kashe wasu matasa biyu, wanda har yanzu ba a san daga inda suka fito ba, kuma aka tafi da wasu wanda suma ba a san yawansu ba, in ban da malamin tsangayar.

Daya daga cikin almajiran malamin da aka sace mai suna Idris Abdulrazak, ya ce, “Muna zaune gaban malam muna karatu sai ga wasu mutane dauke da bindigogi suna harbe-harbe suka shigo suka ce mu kwankwanta.

“Sai suka fito da malamimmu suka tasa shi gaba suka tafi da shi, sai kuma suka kama wasu yara biyu da ke kan babur din roba-roba suka hada su suka yi gaba da su,” inji shi.

Kazalika, wani wanda ’yan bindigar suka je gidansa amma ya nemi a sakaya sunansa ya ce suna shirin kwanciya kenan sai kawai ya ji ana harbi da bindiga, inda ya kira ’yan banga tunda dama suna da lamboninsu sai suka ce basu ba ne.

Hakan a cewarsa ya sa suka gane cewa ’yan bindiga ne, sannan ya kira ’yan a-kaj anguwar tare da jami’an tsaro.

Sai dai ya ce ko kafin su zo har ’yan bindigar sun kashe yara biyu da suka dauko su a kofar gidansa.

Sarkin Wusasa, Isyaku Danlami Yusufu
Sarkin Wusasa, Isyaku Danlami Yusufu

Da yake karin bayani a kan lamarin, Sarkin Wusasa, Isyaku Danlami Yusufu, ya ce ’yan bindigar sun shigo ne da misalin karfe 9:30, amma al’ummar yankin sun sami daukin gaggawa daga jami’an tsaro, sai dai ’yan bindigar sun harbe yara biyu.

Ya ce, “Muna kyauata zaton sun yi musu gardama ne inda daya ya mutu nan take, daya kuma a kan hanyar zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH) da ke Shika.

“Yanzu haka gawarwakinsu na can dan ba a kai ga gane inda suka fito ba, kuma sun tafi da Malam Yakubu Ibrahim Umar, malamin tsangaya, kuma a kwai babura guda biyu da muke kyautata zaton na wadanda suka kashe ne,” inji Sarkin na Wusasa.