✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mutum 9 an jikkata 4 saboda biskit a Jigawa

An yi ta harbi da kibiya tare da ƙona gidaje inda aka halaka rayuwa tara tare da jikkata wasu a ƙananan hukumomin Jahun da Miga…

An tabbatar da rasuwar mutum tara wasu huɗu sun jikkata a wani rikici da ya ɓarke saboda biskit a yankin ƙananan hukumomin Jahun da Miga a Jihar Jigawa.

A ranar Juma’a ne rikicin ya barke bayan mazauna ƙauyen Gululu da ke Ƙaramar Miga sun gano cewa an fasa wani shago an sace biskit mai yawan gaske.

Kakakin ’yan sandan jihar, Lawal Shiisu ya ce mutanen sun yi zargin wasu Fulani ne suka yi satar, har suka bi sahu ɓarayin biskit ɗin zuwa ƙauyen Fulani yankin Yankuna.

Ya ce, “da suka je, sai Fulanin suka hana su shiga ƙauyen inda suka riƙa harbin su da kibiya, inda mutum huɗu suka samu raunuka.

“Wannan ne a cewarsa ya rikiɗe zuwa ƙazamain faɗa inda mutanen suka je suka yiwo gayya, suka far wa matsugunin Fulanin suka riƙa kona gida, lamarin da ya yi ajalin mutum tare tare da jikkata wasu huɗu.

“An kai su asibitoci a ƙananan hukumomin Miga da Jahun inda likitoci suka tabbatar da rasuwar mutane taran,” in ji shi.

Aminiya ta gano cewa bayan faruwar lamarin Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Jigawa, AT Abdullahi da manyan jami’ansa sun kai ziyara wuraren da abin ya faru a Jahun da Miga.

An kuma gudanar da taron masu ruwa da tsaki da nufin samar da zaman lafiya, wanda ya tattaro jami’an gwamnati da sarakunan gargajiya da shugabannin ƙungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah, inda mahalarta taron suka yi kira da a zauna lafiya.

Kakakin rundunar ya ce ƙura ta kafa, amma mutane na zullumi, lamarin da ya sa aka tsaurara matakan tsaro. Ya ƙara da cewa rundunar tana gudanar da bincike kan lamarin.