Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum shida ciki har da wani Limamin coci a wani taron addu’o’i a cikin majami’a, a Dablo da ke arewacin kasar Burkina Faso ranar Lahadin da ta gabata.
A cewar Gidan Radiyon BBC, maharan da adadinsu ya kai 20 zuwa 30 sun cinna wa majami’ar wuta.
Magajin garin, Ousmane Zongo ya ce akwai fargaba, saboda ana kona wasu gine-ginen kuma an far wa wani karamin asibiti.
Tashin hankali dalilin masu ikirarin jihadi ya karu a Burkina Faso tun 2016, kuma wannan ne hari na uku a kan coci cikin makwanni biyar.
Gwamnatin kasar ta bayyana harin na ranar Lahadi a matsayin aikin dabbanci ne na ‘yan ta’adda da nufin wargaza kan al’umma.
Ta kuma yi alkawarin hukunta mutanen da suka kai wannan hari.
Sai dai masu ikirarin jihadin sun gawurta, sojojin kasar sun gaza kare wani makeken sashe na kasar.
A arewacin kasar inda kungiyar Ansarul Islam ke da karfi, sama da makarantu 1,000 sun rufe a ‘yan watannin nan saboda tashe-tashen hankula.
Wasu ‘yan bindiga masu ikirarin jihadi sun kai hari gabashin Burkina Faso, kusa da iyakar kasar Nijar, kuma al-Kaeda da ke da alaka da kungiyar Jama’ar al-Islam wal-Muslimin na ci gaba da zama kalubale a yankin Sahel.