Mutum biyar ne aka tabbatar da mutuwarsu yayin da gidaje da dama suka sha wuta a wani hari da ‘yan bindigar da ba a san ko su waye ba suka kai a kauyen Zangan da ke masarautar Attakar ta karamar hukumar Kaura a Kudancin jihar Kaduna wacce ke kan iyaka da Karamar hukumar Riyom ta jihar Filato.
Shugaban Karamar hukumar Kaura Mista Bege Katuka, a yayin da yake tabbatarwa da manema labarai faruwar lamarin a ranar Juma’a, ya ce maharan sun kai samame ne kauyen ne da misalin karfe 4 na yammacin Alhamis inda suka bude wuta kan mai uwa da wani, abin da ya janyo asarar rayuka mutane biyar.
“Mutane biyar ne suka mutu yayin da wasu mutum biyu kuma suka bace bamu ba a san halin da suke ciki ba tukuna”.
“Sannan sun kona gidaje da dama ciki, har da karamin ofishin ‘yan sanda da aka samar don taimakon tsaro a yankin.” In ji shi.
A karshe shugaban karamar hukumar ya yi kira ga mutanen yankin da su kai hankalinsu nesa domin jami’an tsaro na ci gaba da kokari wajen samar da tsaro a wurin sannan suna ci gaba da gudanar da bincike don zakulo wadanda suka kai harin.
Kauyen Zangan, kamar yadda Aminiya ta ruwaito yana kan iyaka ne da Karamar hukumar Riyom ta jihar Filato inda kwana biyu kafin harin jama’ar Kauyen suka fara bayyana damuwarsu kan kararrakin harbin bindiga da suke ji.
Dukkanin kokarin jin ta bakin Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kaduna DSP Yakubu Sabo ta ci tura domin bai amsa wayar wakilinmu ba kuma bai turo amsar sakon kar ta kwana da ya tura masa ba.