An kashe gomman mutane da safiyar wannan Asabar ɗin a wasu ƙauyuka biyu da ke Karamar Hukumar Mangu ta Jihar Filato.
Wannan lamari dai ya faru ne sakamakon wani mummunan artabu da aka yi tsakanin sojoji da ’yan bindiga, bayan sassauta dokar hana fita ta sa’a 24 da Gwamna Caleb Mutfwang ya yi daga ƙarfe 8 na safe zuwa 4 yamma a yankin.
- Manoma dubu 36 za su ci gajiyar shirin noman Fadama na GO-CARES a Gombe
- Yadda muka fanso ’yan uwan Nabeeha daga masu garkuwa —Dangi
Aminiya ta ruwaito cewa, an kashe akalla ’yan bindiga 30 yayin da wasu sojojin suka jikkata sanadiyyar ba-ta-kashin da aka yi a ƙauyukan Satguru da Tyop.
Wani jami’in tsaro da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce lamarin ya faru a tsakanin ƙarfe 7 zuwa 7:30 yayin da ’yan bindigar masu tarin yawa suka yi wa yankunan da ke titin Gindri ƙawanya.
“Ba tare wata-wata ba aka sanar da sojoji kuma suka tari hanzarin lamarin cikin gaggawa.
“An kashe ’yan bindiga akalla 30 yayin da aka cafke fiye da 50 da bindigogi da sauran makamai.
“Sojoji huɗu sun jikkata,” a cewar jami’in tsaron.
Wata majiya a yankin da ita ma ta buƙaci a sakaya sunanta, ta tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin da cewa “jama’a na cikin zaman ɗarɗar a halin yanzu.
Aminiya ta rashin sa’a a ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar Operation Safe Haven da ke aikin kwantar da tarzoma a yankin.