✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mutum 18 a wani sabon hari a Benuwai

Kakakin 'yan sandan jihar ta ce gawarwakin mutum bakwai kadai aka gano kawo yanzu.

Akalla mutaum 18 ne aka kashe a kauyen Iye da ke Karamar Hukumar Guma a Jihar Benuwai.

Christopher Waku, mai ba da shawara kan harkokin tsaro na Karamar Hukumar Guma, ya ce an kashe akalla mutum 18 a harin.

Waku ya ce, “An kashe mutum 18 a kauyen Iye da ke Karamar Hukumar Guma a jiya (Lahadi) da misalin karfe 6 zuwa 7 na yamma, kauyen na bayan Jami’ar Joseph Sarwuaan Tarka da ke Makurdi (JOSTUM).”

Mazauna yankin sun shaida wa Aminiya cewa an jikkata mutane da dama a harin da aka kai kauyen da almurun ranar Lahadi.

Kakakin ‘yan sandan jihar, Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar harin, inda ta ce an gano gawarwaki mutum bakwai a safiyar ranar Litinin yayin da daya daga cikin maharan kuma ya mutu.