✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mutum 137 a harin Jamhuriyar Nijar

Alkaluma sun nuna mutum 137 ne suka rasu sakamakon harin na Boko Haram.

Sabon rahoto na nuni da cewa akalla mutum 137 ne suka rasu sakamakon harin da aka kai wasu kauyuka da ke kan iyakar Jamhuriyar Nijar da kasar Mali. 

Mayakan Boko Haram sun shiga kauyukan ne a kan babura, suna harbi kan mai uwa da wabi, inji kakakin gwamnatin kasar Abdoulraman Zakaria a ranar Talata.

Sun kai harin ne a kauyukan Intazayene, Bakoarate, Wistane da kuma wasu makotan kauyuka.

A ranar Litinin sojojin Nijar sun gwabza kazamin fada tsakaninsu da mahara a yankin Tahoua, da ke kan iyakar kasar da Mali.

Harin ya yi sanadin mutuwar mutum 40, kamar yadda alkaluma suka nuna.

Amma a safiyar Talata sabon bincike ya gano adadin  mutanen da suka rasun ya kai 137.

Ko a ranar 16 ga watan Maris, 2021, wasu mahara sun hallaka ’yan kasuwa 58 a yankin Tillaberi, kamar yadda sanarwar gwamnatin kasar ta bayyana.