An kashe mutane 11 a rikicin da ya barke tsakanin makiyaya da manoma a kasar Chadi ranar Juma’a.
Rikicin na makiyaya da manoma ya barke a yankin tsakiyar kasar ne ranar Juma’a, tsakanin ’yan gudun hijira da mazauna yankin.
- Yadda manoma 14 suka rasu a hatsarin kwalekwale a Taraba
- Najeriya @62: Jawabin Buhari kan matsalolin Najeriya
A yakin Tsakiya da kuma Kudancin kasar Chadi inda mazauna da dama ke dauke da makamai, ana samun tashe-tashen hankula, inda manoma ke zargin makiyaya da barin dabbobi su yi kiwo a gonakinsu ko kuma su tattake amfanin gona.
Gwamnan Lardin Guera, Sougour Mahamat Galma ya ce, “Manoman sun yi wa makiyaya kwanton bauna ne a lokacin da suke ketarawa ta wani burtali.”
Da farko ya ce mutum tare ne suka mutu a Karamar Hukumar Kouka Margni kafin daga baya a kashe “wasu makiyaya biyu da suka zo da dawakai bayan an yi garkuwa.”
Kimanin motocin ’yan sanda goma da aka tura domin kwantar da tarzoma ne aka harba.
Gwamnan ya ce ya roki sojojin da su kawo musu dauki, saboda fargabar cewa tashin hankalin zai sake dawowa.
A watan Satumba, an kashe mutane 19 tare da raunata 22 a rikicin makiyaya da manoma a Marabe, wani karamin kauye mai tazarar kilomita 500 (mil 310) Kudu maso Gabashin N’Djamena, babban birnin kasar Chadi.
Rikicin ya barke ne zuwa wasu kauyuka biyu da ke makwabtaka da juna kafin ‘yan sanda su samar kwanciyar hankali.
A watan Agusta, an kashe mutane 13 a Gabashin kasar bayan da aka zargi wani yaro da satar fartanyar wani manomi.
Makiyaya daga bangarorin Sahel na Arewacin Chadi suna yawan yin kaura zuwa wurare masu kasa mai albarka inda za su yi kiwon rakuma da tumaki.