✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mutum 1 da yin garkuwa da 3 a Neja

Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta tabbatar da kisan mutum daya da yin garkuwa da mutum uku a Karamar Hukumar Rafi da ke jihar Neja.…

Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta tabbatar da kisan mutum daya da yin garkuwa da mutum uku a Karamar Hukumar Rafi da ke jihar Neja. Jami’in hulda da jama’a ‘yan sandan jihar DSP Abubakar Dan-Ina, ne ya sanar da hakan.

DSP Abubakar, ya ce ’yan bindigar sun kai harin unguwar Kusherki, da misalin karfe 1:00 na tsakar dare ranar Lahadi.

A cewar jami’in, sashen rundunar ‘yan sanda masu yaki da ‘yan fashi da makami na ci gaba da kokarin kubutar da wadanda aka yi garkuwan da su.

Zarnan Kusherki, Alhaji Garba Kusherki, ya ce ‘yan bindigar da adadin su ya kai 20 sun kai harin ne akan babura lokacin da jama’a ke barci.