Gawarwakin akalla mutane 15 ne aka gano a safiyar Alhamis bayan wani hari a unguwar Ugboju da ke Karamar Hukumar Agatu da ke Jihar Binuwe.
Wasu mazauna sun shaida wa Aminiya cewa har yanzu akwai wadanda ba a gani ba, tun bayan harin da aka kai yankin.
Prince Inalegwu Adagole Simon, mazaunin yankin ne, ya shaida mana cewa “da misalin karfe 3 na ranar Laraba ne maharan suka kawo hari suka kashe mutane 15, suka raba wasu da gidajensu.”
Wani mazaunin yankin da ya akwai yiwuwar zuwa da rana a gano karin gawarwakin wasu da ba a gani ba a cikin dajin.
Da yake tabbatar da harin, dan majalisar dokokin jihar Binuwe, Godwin Edoh ya ce, “wannan abun ya girgiza ni a matsayina na wakilin jama’ar wannan yanki, kuma na aika wa gwamna da mataimakinsa hotunan abin da ya faru”
Mazauna yankin sun bayyana cewa kimanin makonni biyu ke nan da maharan suka tsananta kai wa yankin hari.
Kakakin ’yan sandan jihar Binuwe, Catherine Anene, ta ce ba su samu rahoton harin daga DPO mai kula da yankin Agatu ba.
“Sai mun ji daga gare shi,” in ji ta.