✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kashe mayakan Boko Haram 10 a garin Rann

Wannan nasara na zuwa bayan kwana biyu da nada sabon Babban Hafsan Sojin Kasa na kasar.

Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da samun nasarar kashe akalla mayakan Boko Haram 10 daga cikin wadanda suka yi yunkurin kai hari a kan rundunar ‘Operation Hadin Kai’ da ke garin Rann na Karamar Hukumar Kala Balge a Jihar Borno.

Wata sanarwa da Kakakin Rundunar Sojin Kasar, Birgediya-Janar Mohammed Yarima ya fitar a ranar Asabar, ta ce ’yan ta’addan sun kai hari ne dauke da motocin masu bindigogi inda suka yi yunkurin kutsa kai a kofar garin na Rann.

Sanarwar ta ce, “Zaratan dakarun da ke zaune cikin shiri sun yi wa ’yan ta’addan kofar rago kuma suka samu nasarar yi musu mummunan lahani.

“Domin tabbatar da babu sauran wata barazana a garin na Rann, dakarun sun fatattaki ’yan ta’addan har suka tsere suka bar makamansu.

“Sojojin sun yi nasarar lalata daya daga cikin motocin ’yan ta’addan mai dauke da bindiga sannan sun kwato makamai da dama ciki har da bindigar da harbor jirgin sama da bindiga kirar AK-47 guda takwas,” a cewar sanarwar.

Aminiya ta ruwaito cewa, wannan nasarar da rundunar sojin ta samu na zuwa bayan kwana biyu da nada sabon Babban Hafsan Sojin Kasa na kasar.

A ranar Alhamis ce Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Manjo-Janar Farouk Yahaya a matsayin wanda yam aye gurbin marigayi Laftanar-Janar Ibrahim Attahiru, wanda ya rasu a hatsarin jirgin sama tare da wasu manyan da kananan hafsoshin soji goma.