✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe matasa 2 a rikicin kabilanci a Neja

An kona ofishin ’yan sanda da banka wa Fadar Sarkin garin wuta.

Rikicin kabilanci ya yi ajalin wasu matasa biyu a garin Salka da ke Karamar Hukumar Magama ta Jihar Neja.

Bayanai sun ce rikicin ya barke ne a tsakanin wasu matasan kabilar Kambari da kuma wasu matasan kabilar Fulani a garin na Salka.

A wata sanarwa da kakakin ’yan sandan Jihar Neja, Wasiu Abiodun ya raba wa manema labarai, ya ce harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyu tare da yin garkuwa da mutane takwas ciki har da wani jami’in kiwon lafiya.

Bayanai dai sun nuna cewa lamarin ya yi sanadiyar kona ofishin ’yan sanda da banka wa Fadar Sarkin garin wuta da kuma wasu gidajen Fulani a yankin.

Alhaji Abubakar Suleman Abara, Dagacin Salka da aka kona fadarsa, ya ce har ya zuwa Yammacin ranar Talata suna cikin wani yanayi na tashin hankali.

Bala Tajir Salka, Dan Galadiman Salka, ya ce rashin fahimtar juna ce aka samu a tsakanin matasan Fulanin da kuma na kabilar Kambari da ta janyo lamarin.

A yanzu haka dai Gwamnatin jihar na ci gaba da fadi-tashin shawo kan rikicin kabilanci da ya barke.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Ahmed Ibrahim Matane, ya ce duk da yake ya zuwa yanzu ba su gama tantance yawan asarar da aka yi ba, amma sun tura karin jami’an tsaro a yankin domin kwantar da tarzoma da kuma dawo da zaman lafiya.

A wani labarin mai nasaba da wannan, rundunar ’yan sanda ta Jihar Nejan ta tabbatar da cewa wasu ’yan bindiga sun kai hari a wani asibitin gwamnati dake garin Gulu na yankin Karamar Hukumar Lapai.

Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Jihar Neja, Mista Emmanuel Umar ya ce an tura karin jami’an tsaro a yankin na Gulu.