Wasu ‘yan daba da ba a san ko su wane ne ba sun hallaka mataimakin kwamishinan ‘yan sandan Jihar Borno a jiharsa ta Kuros Riba.
Wata majiya ta ce wasu da ake zargin ‘yan daba ne suka kashe dan sandan mai suna ACP Egbe Eko Edum, yayin da ya je jiharsa ta Kuros Riba domin ziyartar ‘yan uwansa, a daidai lokacin da motarsa ta lalace a kan titi.
- Ya kamata a yi amfani da sojojin haya wajen yaki da ‘yan ta’adda – Gwamnoni
- Dalilin da ya sa muka kashe Manoma 78 a jihar Borno — Abubakar Shekau
- Fusatattun matasa sun banka wa Sarakunan su wuta a Kuros Riba
Tun da farko dai sai da ACP Egbe ya kira mai dakinsa kan ta je ta dauke shi lokacin da motar tasa ta samu matsala, sai dai ko kafin ta karasa wurin tuni ‘yan daban suka suka far masa har sai da rai ya yi halinsa.
Rundunar ‘yan sandan jihar ce ta tabbatar da mutuwar ACP Egbe, wanda shi ne kwamandan rundunar 73 PMF Squadron da ke Magumeri a Maiduguri ta Jihar Borno.
Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan jihar, Irene Ugbo ta ce lamarin ya faru da misalin karfe 1:00 na daren Talata a kan Titin Murtala Mohammed dake Kalaba.
Irene ta kuma ce tuni suka fara gabatar da bincike kan faruwar lamarin sun kuma kai gawarsa dakin adana gawawwaki a asibiti.