✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kashe manoma biyu a Taraba

Karar kwana ta cimma manoman ne yayin da suka fita aikin girbin amfanin gonarsu.

Ana fargabar cewa ’yan bindiga sun kashe wasu manoma biyu suna tsaka da aiki a gonakinsu a Karamar Hukumar Yangtu a Jihar Taraba.

Lamarin, a cewar wata majiya a yankin, an kashe manoman ne a gonarsu da safiyar ranar Talata.

Majiyar ta bayyana cewa, karar kwana ta cimma manoman ne yayin da suka fita aikin girbin amfanin gonarsu da ke kauyen Kwambai wanda ya yi iyaka da kananan hukumomin Ussa da Yangtu.

Aminiya ta ruwaito cewa, kisan manoman na zuwa ne kwanaki uku bayan kashe wasu manoma 10 da ake zargin wasu makiyaya sun yi a yankin.

Sai dai mai magana da yawun ’yan sandan jihar, SP Usman Abdullahi ya shaida wa wakilinmu cewa bai samu rahoton faruwar lamarin ba.