✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kashe makiyaya 10 da suka je radin suna a Binuwe

Wasu gungun ’yan daba sun kashe matafiya 10 a kauyen Yelwata da ke tsakanin iyakar jihohin Binuwe da Nasarawa da ke kan babbar hanyar Lafiya…

Wasu gungun ’yan daba sun kashe matafiya 10 a kauyen Yelwata da ke tsakanin iyakar jihohin Binuwe da Nasarawa da ke kan babbar hanyar Lafiya zuwa Makurdi.
 
Shugaban kungiyar Miyetti Allah, Alhaji Danladi Chiroma shi ne ya fada wa wakilinmu cewa makiyayan mazauna garin Awe ne da ke jihar Nasarawa da suke kan hanyarsu da yammaci ranar Asabar za su halarci radin suna a wani wuri.
 
Ciroma ya ce motar da suke tafiya da ita ta lalace a kauyen Yelwata sai direban ya sauko yana kokarin gyarawa sai kawai ’yan dabar suka dirar musu da muggan makamai.
 
Ya ce sun gano tare da mika gawarwakin mutum shida daga cikin mutum 10 da aka kashe ga ’yan sanda sannan kuma direban motar wanda Bahushe ne ya tsira.
 
Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto rundunar ’yan sandan jihar Binuwe ba ta amsa wayar da aka buga mata ba kuma ba ta amsa sakon wayar da aka aika mata ba