An yi wa wata dattijuwa Hajiya Amina mai shekaru 90 mummunan kisan gilla tare da jikarta Bilkisu mai shekaru 23 a Unguwar Tudun Wada da ke garin Daura a Jihar Katsina.
Bayanai sun ce an kashe dattijuwar ta hanyar maƙara yayin da ita kuma jikarta aka yi mata yankan rago ranar Alhamis a gidansu da ke bayan Tashar Kudu a garin na Daura.
Haka kuma, wani mazaunin Daura ya shaida wa Aminiya cewa, maharan sun feɗe cikin jikar sannan suka yanke ƙodarta.
Wannan dai na zuwa ne yayin da bayan nan wasu matasa suka kai farmaki gidan mamatan inda suka yi awon gaba da wani akwatin talabijin da ke gidan kirar Plasma.
An ruwaito cewa mamatan sun kai korafi kan faruwar lamarin wanda ’yan sanda ke gudanar da bincike a kansa yayin da wannan mummunan ya auku.
“An gano akwatin talabijin din yayin da wannan mummunan lamari ya auku a daidai lokacin da ake ci gaba da bincike.
“Sai dai har yanzu ba a gano ko wadanda suka ɗauki akwatin talabijin din na da hannu a wannan kisan gillar ba,” a cewar majiyar.
Gwamnan Katsina Dikko Umar Radda ya jajanta wa ’yan uwan mamatan da kuma Masarautar Daura dangane da faruwar wannan lamari.
Jami’in hulɗa da al’umma na rundunar ’yan sandan Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu wanda Aminiya ta tuntuba ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai bai yi wani ƙarin haske ba.