Majiyoyi da dama sun tabbatar da cewa an kashe jagoran reshen Afirka ta Yamma na kungiyar ISIS, wato ISWAP, Abu Musab Al-Barnawi.
Jaridar Daily Trust ta bayar da rahoton cewa an kashe shi ne a karshen watan Agustan bana.
- Yadda Aka Ceto Mutum 638 Da Ake ‘Bautarwa’ A Arewacin Najeriya
- Mahara Sun Kashe Soja, Sun Sace Yara A Zariya
Al-Barnawi dai dan Muhammad Yusuf, mutumin da ya kirkiri kungiyar Boko Haram, ne.
A 2009 jami’an tsaro suka kashe mahaifin lokacin da kungiyar ta fara yakar hukumomin Najeriya.
Yadda aka kashe shi
Akwai ruwayoyi biyu a kan yadda aka kashe Al-Barnawi.
Wata ruwayar ta ce sojojin Najeriya ne suka kashe shi, yayin da dayar kuma ta ce ya mutu ne yayin wani fadan cikin gida a tsakanin wasu bangarori na kungiyar ta ISWAP da ba sa ga maciji da juna.
Ruwaya ta farko dai ta ta’allaka ne a kan wani bayani da wasu jami’an tsaro a bakin daga suke yadawa a tsakaninsu, wanda ke nuna cewa wani kwanton-bauna sojoji suka yi da ya kai ga kashe shi da wasu manyan kwamandojin ISWAP biyar da ma mayaka da dama wadanda suka yi masa mubaya’a.
Wata majiya ta ce an kashe shi ne a Bula Yobe, wani gari da ke kusa da iyakar jihohin Borno da Yobe a tsakanin Mobbar da Abadam.
Amma wasu majiyoyin sun shaida wa Daily Trust cewa rikicin shugabanci ne ya yi ajalin Al-Barnawi.
Daya daga cikin majiyoyin ta ce rigimar ta kai kololuwa ne a tsakanin 14 da 26 ga watan Agusta, kuma rikicin ya lakume rayukan kwamandoji da dama a bangarorin biyu.
Sai dai kuma wata majiyar ta ce daya bangaren ne ya yo hayar ’yan ta’adda daga yankin Afirka ta Tsakiya da nufin hambarar da Al-Barnawi, kuma ya yi nasara.
Tashen Al-Barnawi
A shekarar 2016 kungiyar ISIS ta sanar da nadin Al-Barnawi a matsayin jagoran reshenta na Afirka ta Yamma, Boko Haram, wadda a lokacin ke karkashin jagorancin Abubakar Shekau, wanda ya yi mubaya’a ga kungiyar ta ISIS a 2015.
Wannan lamari ne ya fito da Al-Barnawi, wanda matashi ne, sannan ya haifar da darewar kungiyar gida biyu.
An dai ce daya daga cikin dalilan da suka sa ISIS ta tsige Shekau daga jagoranci shi ne don ta ladabtar da shi bisa “saba sanannun hukunce-hukunce”, sai kuma fatan samun goyon bayan mayakan Boko Haram mabiya Muhammad Yusuf, yayin da kungiyar ke fuskantar barazana daga wasu kungiyoyin.
Shi dai Shekau ya karbi ragamar kungiyar ne bayan mutuwar Muhammad Yusuf a 2009.
Martanin sojin Najeriya
Ba kasafai hafsoshin rundunar sojin Najeriya kan gaskata ko karyata labarin kisan manyan kwamandojin Boko Haram ko ISWAP ba.
Wannan ba ya rasa nasaba da yadda aka yi ta ba da sanarwar kashe Abubakar Shekau, amma daga bisani sai a ji shi ya dawo.
Sai a watan Mayun 2021 ne dai ya kashe kanshi bayan da mabiyansa suka yi gumurzu da mayakan ISWAP a maboyarsa da ke Dajin Sambisa.
Da aka tuntube shi game da batun, Daraktan Yada Labarai na Rundunar Sojin Najeriya, Manjo Janar Benjamin Sawyer, ya shaida wa wakilin Daily Trust cewa ba zai iya tabbatar da lokacin da aka kashe Al-Barnawi ba, saboda sojoji ba su da alaka da ’yan Boko Haram.
“Idan akwai matsala a tsakanin ’yan Boko Haram yaya za a yi na sani?
“Bisa al’ada mukan samu bayanai game da yaki da ta’addanci duk mako biyu; idan ’yan ISWAP ko ’yan Boko Haram na fada a tsakaninsu galibi ’yan jarida ne ke ba al’ummar kasa labari ba mu ba, tun da ba a sansaninsu muke ba”, inji Janar Sawyer.
Makashin maza…
Al-Barnawi dai ya riga mu gidan gaskiya ne kasa da wata biyu bayan ya kammala tattare komai a hanninsa sakamakon mutuwar Abubakar Shekau.
A wani sakon murya da ya nada a harshen Kanuri a lokacin, ya tabbatar da mutuwar Shekau da kuma nasarar bangarensa.
Ga ma abin da yake cewa a sakon na minti 28:
“Ko a mafarki, Shekau bai taba tsammanin haka zai faru da shi ba, amma da karfin Ikon Allah mun hargitsa masa lissafi.
“Ya kidime ya tsere xuwa cikin daji inda ya kwana biyar yana watangaririya.
“Mun bi shi, inda muka tunkare shi da ruwan wuta, sai ya tsere.
“Daga nan dakarunmu suka yi kira a gare shi ya mika wuya saboda a ladabtar da shi.
“Mun yi ta ba shi tabbacin cewa ba mu da niyyar kashe shi amma ya rude ya tsaya kai da fata.
“Mutum ne mai taurin kai, don haka ya gwammace yam utu da ya ba da kai”.