✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kashe fararen hula 17,831 daga fara yakin Ukraine zuwa yanzu – MDD

Hukumar ta tattara alkaluman ne daga watan Fabrairu zuwa Disamba

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai Kula da Kare Hakkin Dan Adam (OHCHR) ya ce yawan fararen hular da aka kashe daga fara yakin Ukraine zuwa yanzu ya kai 17,831.

Hukumar ta ce ta tattara alkaluman ne daga ranar 24 ga watan Fabrairu zuwa 26 ga watan Disamban 2022.

A cewar hukumar, daga cikin adadin, an kashe fararen hula 6,884, wadanda suka hada da maza 2,719 da mata 1,832 da yaran mata 175 da kuma yara maza 216 da kananan yara 38.

Kazalika, alkaluman sun nuna akwai manyan mutane 1,904 da ba a kai ga tantance jinsinsu ba kawo yanzu.

Hukumar ta kuma ce an jikkata jimlar mutum 10,947, inda galibinsu suke zaune a yankunan Donetsk da Luhansk, inda aka kashe mutum 4,052 sannan aka jikkata wasu 5,643.

Ofishin ya kuma yi gargadin cewa, “Asalin yawan mutanen zai iya haura haka saboda alkaluman da muke tattarawa daga yankuna inda ba a samun cikakkun bayanai a kan lokaci.”

Yanzu dai kimanin kwanaki 308 ke na cif tun da kasar Rasha ta kaddamar da hare-hare a kan kasar ta Ukraine.