✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kashe fararen hula 173 a wata hudu a Sudan ta Kudu —MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane 173 aka kashe sakamakon tashe-tashen hankula a kasar Sudan ta Kudu a watanni hudu.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane 173 aka kashe sakamakon tashe-tashen hankula a kasar Sudan ta Kudu a watanni hudu.

Majlaisar Dinkin Duniyar ta bayyana cewa cin zarafin bil Adama na hauhawa tsawon wannan wa’adin a sassan kasar.

Ta bayyana hakan ne a wani rahotonta na hadin gwiwa da Ofishin Babban Kwamishinan Kara Hakkin Dan Adam na Majalisar (OHCHR), inda ya ce ana cin zarfi  tare da take hakkin dan Adam duk sa’a guda, sakamakon rikicin da kasar ke fama da shi.

Rahoton wanda ya kunshi bayanan da aka tattaro tun daga 11 ga watan Fabrairu zuwa 31 ga watan Mayu, an gudanar da shi ne a kananan hukumomin Koch Leer da Mayendit da kuma makwabtansu.

Rikicin dai ya raba akalla fararen hula 44,000 a kauyuka 26 da gidajensu.

Baya ga wadanda aka kashe, rikicin ya shafi akalla kauyuka 28 tare da jikkata mutane 12 gami da sace mata 37 da kananan yara.

Rahot0n ya nuna yawancin wadanda aka sace sun fuskanci cin zarafi ta hanyar fyade, ciki har da yara ’yan kasa da shekaru takwas.

Jimillar laifuka 131 na fyade dai da majalisar ta ce ta tattaro, sai kuma wadanda aka yi wa fiye da sau daya da maza daban-daban, ciki har da wata yarinya ’yar shekara tara da har sai da ta mutu.

Majalisar Dinkin Duniyar ta dora laifin kan wasu bata-garin jami’an tsaron hadin guiwa da ta masu tada kayar baya da ke aiki karkashin jami’an Karamar Hukumar Koch da Mayendit, wandda ta ce sun fi aikata laifukan take hakkin dan Adam da cin zarafin.

Shugaban Ofishin Jakadancin MDD, Janar Nicholas Haysom, ya ce kawo yanzu babu wanda aka yanke wa hukunci daga cikin masu aika duk wadannan laifukan.

“Gwamnati tana da hakki a karkashin dokokin kasa da kasa don kare fararen hula.

“Tilas ne ta binciko zarge-zargen take hakin bil Adama da kuma hukunta wadanda ake zargi da aikata laifin bisa bin ka’idojin shari’a,” in ji shi.